Ibrahima yakubu
Bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a birnin Landan a ranar Lahadi, shugabannin kungiyar Buzaye ta Najeriya sun mika sakon ta’aziyya.
Shugaban kungiyar haɗin kan al’ummar Buzaye mazauna Najeriya, Alhaji Ali Muhammed Agadez, ya mika sakon ta’aziyya ga daukacin al’ummar Najeriya bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasa.

A cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a yau Talata, bayan kammala jana’izar marigayin, Alhaji Ali Agadez ya bayyana jimaminsa bisa samun labarin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, inda ya yi masa addu’ar Allah ya jikansa da rahama.
Alhaji Ali ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga daukacin iyalan marigayin, tsohon shugaban Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari, da kuma ga al’ummar Najeriya baki ɗaya.
Ya ce, “Mun yi babban rashi a wannan lokaci. Saboda haka muke mika wannan gaisuwar ta’aziyya tare da fatan alheri da addu’ar Allah ya jikansa da rahama.”
Ya ci gaba da cewa: “Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, da kuma ga gwamnatin da al’ummar ƙasar. Muna tare da ku a wannan lokaci na bakin ciki.”
Ali ya ƙara da cewa suna amfani da wannan dama wajen jajantawa daukacin al’ummar Najeriya bisa wannan babban rashi na ubanmu, shugaban al’umma da babban jagora.
Alhaji Ali Muhammed Agadez ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin jajirtaccen shugaba mai kishin cigaban Afrika baki ɗaya, da fatan kyautatuwar al’amura a nahiyar.
Ya kuma bayyana rasuwar Muhammadu Buhari a matsayin mai matuƙar ratsa zuciya, kuma babban rashi ne ga Najeriya da sauran ƙasashen Nahiyar Afrika gaba ɗaya.

Ya kuma bukaci Yan Nigeria da jamhoriyar Nijar su ci gaba da yiwa kasashen Addu’o’in zaman kyautata zamantakewa da dankwan zumunci domin bunkasar tattalin arziki da ci gaban daukacin alumman kasashen


















